ABNA24 : Kwamitin sojojin dake rike da mulki ya bayyana hakan ne bayan taron tuntuba na tsawon kwanaki uku da aka kammala a jiya Asabar.
Da yake sanar da hakan shugaban kwamitin sojojin Kanal Assimi Goita, ya ce zasuyi duk iya kokarinsu na aiwatar da duk kudurorin da suka cimma saboda makomar kasar da al’ummarta.
Mali : An Fara Taron Tuntuba Game da Shirin Kafa Gwamnatin Riko
A saboda haka a cewarsa, suna fata da kuma bukatar hadin kan duniya domin tafiyar da wannan mulkin rikon kwarya yadda ya kamata.
A cen baya dai kungiyar ECOWAS, ta bukaci sojojin da su mika mulkin rikon kwarya ga farar hula a cikin wa’adi na akalla shekara guda.
Kungiyar ta ECOWAS wacce ta kakaba wa Malin takunkumin tattalin arziki da kudi, ta baiwa sojojin har zuwa ranar Talata domin nada shugaba da firaministan riko fararen hula.
An Zabi Shugaban Ghana A Matsayin Sabon Shugaban ECOWAS
A wani lokaci a ranar A Talata ne ake sa ran wasu manyan sojojin na Mali, zasu isa birnin Accra inda zasu gana da shugabannin da gwamnatocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammcin Afrika na Ecowas wadanda zasuyi taro a Ghana, kamar yadda wata majiya kusa da mai shiga tsakanin na kungiyar ta ECOWAS, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonatan ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.
342/